Home Siyasa Babu abinda Buhari ya yi sai jagwalgwala Najeriya — PDP

Babu abinda Buhari ya yi sai jagwalgwala Najeriya — PDP

0
Babu abinda Buhari ya yi sai jagwalgwala Najeriya — PDP

 

 

 

Babbar Jam’iyar adawa ta ƙasa, PDP ta bayyana rashin gamsuwa tare da damuwa a kan yadda Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya “jagwalgwala al’amura a Najeriya”.

Jam’iyar ta ƙara da cewa Buhari ya yi watsi da muhimman shawarwari na samarwa kasa mafita, da rashin daukar mataki na ceto rayuka da dukiyoyin al’umma da ke salwanta dare da rana a cikin kasa.

Shugaban jam’iyar PDP na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu ne ya fadi hakan a jiya Lahadi a birnin Makurdi, Jihar Binuwai, a lokacin gudanar da taron taya shi murnar zama shugaban jam’iyar adawa na kasa, wanda gwamnati da al’ummar jihar, karkashin jagorancin Gwamnan Samuel Ortom su ka shirya masa.

Ayu ya ce, hakika ko shakka babu, sakacin Buhari dangane da dacewa ya dauki matakai masu tsauri don kawo karshen matsalar tsaro da sauran kalubale na daga cikin dalilan da zai sanya ƴan Nijeriya su amince cewa Shugaban Kasan ba shi da dabara ko karfin halin gyaran matsalolin kasar nan.

“Kisan gilla na ganganci da cin amana irin wanda aka yiwa wasu mutane a Sokoto da na Kaduna, da kisan Kwamishina a mahaifar shugaban kasa da ke Katsina, da wasu sauran hare-hare na fitar hankali da a keyi ana satar jama’a ko yi wa mata fyade da sauran irinsu, duk sun tabbatar da rashin adalci, da iya jagoranci na Shugaban Kasa Buhari, da wadanda ya baiwa amanar kiyaye rayukan al’umma.

“Dole ne mu gaya wa Shugaban Kasa cewar, ya tashi tsaye ya rufe ido, ba sani ba sabo, yayi gyara a kan matsalar da kasa take ciki; domin kuwa ana daukar rayuka al’umma ana kisan gilla tamkar kiyashi, abin da ya sanya tsoro da fargaba da rashin tabbas a zukatan al’umma, mussaman talakawa wadanda basu ci basu sha ba,”
Inji Sanata Iyorchia Ayu.

Ya kuma roki ƴan Nijeriya da kada su karaya a kan sake gina kasa mai albarka da nagarta da zaman lafiya, muddin a ka samu kyakyawan shugabanci nagari mai gaskiya da adalci ga al’umma.

Ya ce, “kuskure ne ayi zancen wargajewar Nijeriya sabo da wadanan kalubalen, don kuwa jam’iyyar PDP tana iya kokarin da take yi na sake ceto da gina kasa don amfani al’umma a gobe da zasu cimma burinsu na tabbatar zaman lafiya da rayuwa mai albarka da adalci.”

Ayu ya kuma roki al’umma da su ci gaba da yi wa Nijeriya fatan alheri da neman hadin kai da uzuri ga lamuran da za su kara karfafa gaskiya, zaman lafiya da fahimtar juna a tsakani.