
Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, CBN Godwin Emefiele ya ce babu bukatar sake ƙara wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 na daina karɓar tsoffin kuɗi.
Gwamnan babban bankin ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kai ma’aikatar harkokin wajen kasar domin tattaunawa kan manufar sake fasalin kudi a kasar.
Mista Emefiele ya ce: “Al’amarin ya lafa sosai tun lokacin da aka fara biyan kudade a kan kanta domin rage cinkoso a guraren ATM.
“Saboda haka, babu bukatar sake daga wa’adin daga ranar 10 ga Fabrairu.”
Shugaban babban bankin ya kuma ce bankin zai sa kafar wando daya da masu POS da ke karbar sama da N200 na ganin cirar kuɗi.