
Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce al’ummar Kudu-maso-Gabas ba su da wani dalilin da zai hana su zaɓa4 jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.
Atiku ya yi magana ne a dandalin Ndubusi Kanu, Owerri yayin taron gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na PDP a jiya Asabar.
Dalilinsa shi ne, zai zauna ya saurari ‘yan kabilar Igbo da ke kan gaba wajen fafutukar sake fasalin kasar.
Ya kuma yi alkawarin zuba dala biliyan 10 ga ‘yan kasuwa a kasar Igbo domin bunkasa harkokinsu na kasuwanci da tattalin arziki a matsayin mutanen da aka sansu da kasuwanci.
“Idan ni ne shugaban kasa, to kuwa Imo na fadar shugaban kasa. Mun san muna da kalubalen tsaro a Imo da duk fadin kasar nan. Amma da zarar an zabe ni Shugaban kasa, zan zauna da ku don magance matsalar. Ina da alaka da Igbo shekaru da dama.
“Na san Igbo ƴan kasuwa ne. Idan aka zabe ni zan dawo da kasuwanci a kasar Igbo. Da zarar an zabe ni, zan zuba dala biliyan 10 kan kananan sana’o’i a kasar Igbo; da wannan, babu wanda zai ce ba shi da wani abin yi a Kudu-maso-Gabas,” in ji Atiku