Home Kanun Labarai Babu laifinmu a wahalar man fetur da a ke yi a ƙasa: IPMAN

Babu laifinmu a wahalar man fetur da a ke yi a ƙasa: IPMAN

0
Babu laifinmu a wahalar man fetur da a ke yi a ƙasa: IPMAN

Kungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN, ta fitar ce ba laifinta ba ne a karancin man fetur da ake fama da shi a ƙasa.

Kungiyar ta kuma ce mambobinta ba su da hannu a karancin da ake fama da shi a halin yanzu.

Femi Adelaja, Shugaban IPMAN ta defot ɗin Mosinmi a Jihar Ogun, a wata sanarwa da ya fitar a karshen mako, ya ce babu man fetur a cikin gidajen man fetur na kasa (NNPC) a fadin Nijeriya.

Ya ce a yanzu haka farashin man fetur daga defot ya kai Naira 220 a fadin gidajen man da ke Legas.

A cewarsa, ‘yan kasuwan sun koma siyan kayan ne daga defot defot na masu zaman kansu, inda suke sayar da kayan a farashi mai tsada.

Don haka ya danganta matsalar karancin man da ake fama da ita a halin yanzu ga gwamnatin tarayya da kuma gazawar kamfanin man fetur na kasa (NNPC) wajen samar da man ga mambobinsa a farashi mai sauki.