
Alhaji Sule Lamido tsohon Gwamnan jihar Jigawa a karkashin tutar jam’iyyar PDP, kuma mai neman zama dan takarar PDP a zaben Shugaban kasa da za ai nan gaba, ya bayyana cewar babu wani mahaluki da ya isa ya hana shi zama Shugaban Najeriya na gaba.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a karamar hukumarsa ta Birnin-Kudu a jihar Jigawa, yace babu wata masin lamba da zata iya hana masa zama Shugaban kasa, idan Allah ya lamunce masa.
Ya bayyana cewar, babu ko tantama za’a yi zaben 2019 tsakanin Musulmi ‘yan Arewa guda biyu, inda yace dukkansu sun taba rike mukamin Gwamna da kuma Minista a zamanin da suka yi mulki a mabambantan lokuta.
Babu wani mahalukin da ya isa ya hana ikon ALlah, idan har ya amince cewar ni Sule Lamido zan zama Shugaban Najeriya, babu wanda ya isa ya hanani sai na zama duk kuwa irin kitimurmura da kutunguila da za’a shirya min sai na zama.
“Babu ko shakka cewar, a shekarar zabe ta 2019, za’a kara ne tsakanin Fulani Musulmi guda biyu ‘yan Arewa, kuma duk sun taba zama Gwamna da kuma Minista”
“Bambancin da yake tsakanina da Buhari shi ne, duk da cewar ya taba zama Gwamna lokacin mulkin soja, amma bai taba yiwa al’umma hidima ba, ya taba zama ministan albarkatun man fetur, na san da yawa basu sani ba. Lokacin da na zama Ministan harkokin wajen Najeriya, babu wanda bai san waye ni ba duk duniya, haka kuma zama na Gwamna kadai ya isa yasa a san waye ni”
Sule Lamido ya kara da cewar, Buhari Bafulatani ne kawai a suna, amma ba zai iya hada ko da jumla guda daya cikin harshen Fulatanci ba.
“Buhari da jam’iyyun adawa a bayan sun sha gayawa mutane karya kan zaben 2015,amma yanzu mutane sun gama fahimtar su waye su, don haka ba wanda zai kuma yadda da su a zaben 2019”
“Babu abinda wannan Gwamnatin da jam’iyyar APC suka iya sai fancale da bata suna”