Home Kanun Labarai Babu wanda ya taɓa hana Shugaba Buhari zuwa Amurka, abinda Atiku Abubakar ya faɗa sam ba gaskiya ba ne – Fadar Shugaban ƙasa

Babu wanda ya taɓa hana Shugaba Buhari zuwa Amurka, abinda Atiku Abubakar ya faɗa sam ba gaskiya ba ne – Fadar Shugaban ƙasa

0
Babu wanda ya taɓa hana Shugaba Buhari zuwa Amurka, abinda Atiku Abubakar ya faɗa sam ba gaskiya ba ne – Fadar Shugaban  ƙasa
Nigeria's President Muhammadu Buhari addresses a Franco-Nigerian business forum at French employer association Medef's headquarters in Paris on September 15, 2015. AFP PHOTO / ERIC PIERMONT (Photo credit should read ERIC PIERMONT/AFP/Getty Images)

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a zantawar da aka yi da shi ranar Asabar, yayi zargin cewar an taba hana Shugaba Buhari zuwa kasar Amurka har na tsawon Shekaru 15, sabida batun addini.

Wannan abin da Atiku Abubakar ya fada, sam ba gaskiya bane, karya ce tsagwaronta, akwai abin takaici kwarai da gaske, mutum kamarsa, da ya taba zama mutum na biyu a najeriya ya zauna yana kitsa zancen da ba gaskiya bane.”

“Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ko kafin ya hau kan kujerar shugabancin najeriya, babu inda aka taba ruwaito cewar an hana shi zuwa kasar Amurka, bama Amerika, babu wata kasa a duniya da aka taba haramta masa shigarta”

“A ko da yaushe, kasashen duniya suna mutunta Shugaba Buhari duk inda yaje, suna farin ciki idan sun ganshi, babu inda yaje da ba’a karbe shi da mutuntawa ba, tun kafin ya zama Shugaban kasa, irin wannan mutuntawa ita ce ake yi masa har yanzu”

“Atiku Abubakar kawai yana kauce kauce ne, akan tambayar da aka yi masa na kasa shiga kasar Amurka da yayi na fiye da shekaru goma, mai makon ya bayar da amsa, sai ya tsaya yin kazafin cewar, ai Buhari ma an hana shi zuwa Amurka”

Idan Atiku Abubakar yana da matsala da hukumomin kasar Amurka, yana iya bin hanyoyin da suka dace ya gyara tsakaninsa da su, ba sai ya yiwa Shugaban kasa kazafin cewar, an hana shi shiga kasar Amurka na tsawon shekaru 15 ba, kafin zamansa Shugaban najeriya.

Babban mai taimakawa Shugaban kasa na musamman akan harkokin yada labarai femi Adeshina ne ya fitar da wannan martani a madadin fadar Shugaban kasa a shafinsa na facebook, a ranar Asabar, a yayin da Shugaba Buhari ke halartar wani muhimmin taro a kasar Jordan.