Home Labarai Babu wani ci gaba a kare hakkin ɗan-ƙasa a mulkin Tinubu — Amnesty

Babu wani ci gaba a kare hakkin ɗan-ƙasa a mulkin Tinubu — Amnesty

0
Babu wani ci gaba a kare hakkin ɗan-ƙasa a mulkin Tinubu — Amnesty

Daraktan kungiyar yaki da yayye hakkin dan adam, Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce babu wani gagarumin ci gaba da aka samu wajen kare hakkin bil’adama a gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanusi, wanda ya bayyana hakan a wata hira da gidan rediyon DW Hausa a jiya Lahadi, ya gabatar da hujjar sa kan gazawar gwamnati wajen gudanar da bincike kan take hakkin bil’adama da aka yi a baya da kuma rashin yin kataɓus ga cin zarafin da ke ci gaba da gudana.

Ya kuma soki yadda gwamnati ke dogaro da fitar da sanarwar manema labarai a matsayin mataki ga irin wadannan abubuwa, yana mai cewa, wannan magana ce kawai ta rashin inganci na gwamnatin da ta gabata.

Ya ce, “Gaskiya babu wani haske, sai dai ma fargaba. Na farko, gwamnati mai ci ba ta nuna wani kuduri na bincike kan take hakkin dan Adam a baya ba.

“Na biyu, a farkon wannan gwamnatin, an kashe akalla mutane 200, matakin da gwamnati ta dauka kan take hakkin dan Adam a karkashin shugaban kasa mai ci ya yi kama da rashin tsarin gwamnatin da ta shude, ta dogara da fitar da bayanai kawai na. Wannan rashin daukar matakin na kara rura wutar rashin ci gaba mai ma’ana.

Ya lura cewa tarihin take hakkin Najeriya ya samo asali ne tun lokacin turawan mulkin mallaka.