Home Labarai Babu wata matsala tsakanina da Nuhu Gidado – Gwamna MA Abubakar

Babu wata matsala tsakanina da Nuhu Gidado – Gwamna MA Abubakar

0
Babu wata matsala tsakanina da Nuhu Gidado – Gwamna MA Abubakar

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya musanta zargin da akai masa na mayar da tsohon mataimakinsa saniyar ware a harkar Gwamnati, dalilin da ya sanya wasu ke ganin tsohon mataimakin Gwamnan yayi murabus daga mukamin nasa.

Gwamna MA ya bayyana cewar, shi dai a iya saninsa babu wani abu da akaiwa tsohon mataimakin Gwamnan na ware shi ko yin Gwamnati ba tare da shi ba.

“Sau biyu ina tafiya hutu tun zama na Gwamnan Bauchi, kuma duk lokacin da na tafi zan aikawa majalisar dokoki takarda na kuma bashi rikon ragamar tafiyar da jihar ta Bauchi a hannunsa”

‘A saboda haka ba gaskiya bane wani ya fito yace akwai jikakkiya ko tsamin dangantaka tsakanina da shi (Nuhu Gidado)”