
Daga Abba Wada Gwale
Sanata Isa Misau ya zargi Babban Sufeton ’Yan Sandar ƙasar nan Ibrahim Idris da yiwa wata ‘yar sanda ciki.
A cewar sanatan, babban sufeton ’yan sandar daga baya ya auri wannan ’yar sanda mai suna Esther kuma mai rike da mukamin DSP a ranar 15 ga watan Satumbar da ya gabata a garin Kaduna.
Da ya ke maƙala a zauren Majalisar Dattawa a yau Laraba, sanatan ya ce a yanzu haka Esther na dauƙe da ciki wata huɗu.
Ya ƙara da cewa Ibrahim Idris ya yi ƙarin matsayi ga Esther da kuma wata Amina wacce ita ma sanatan ya ce farkar babban sufeton ’yan sandar ce.
A cewar Sanata Misau, waddannan matan ba su cancanci ƙarin matsayin da ya yi musu ba.
“Wannan halayya ta shugaban ‘yan sandar ƙasar nan ta saɓawa doka. Domin kuwa dokar aikin ɗan sanda ta hana ɗan sanda ya auri ’yar sanda,” inji sanatan.
Daga nan ne Shugaban Majalisar Dattawan Bukola Saraki ya kafa wani kwamitin wucin gadi don binkicen wannan bahallatsar.
Sanatan dai ya jima yana takun saka da babban sufeton ’yan sandar, yanda a can baya ya zarge shi da yi wa wasu shafaffu da mai ƙarin matsayi da kuma karbar togaciya wajen kamfanonin mai.