
Kwamishinan ƴan Sanda, CP, a jihar Enugu, Ahmed Ammani, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wani mataimakin Sufetan ‘yan sanda, ASP, kan zargin yi wa wata ƴar shekara 17 da ke tsare fyaɗe.
ASP ɗin yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Awgu da ke jihar Enugu.
Umurnin binciken na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe ya fitar a Enugu a yau Asabar.
Kwamishinan ya umarci sashen binciken sirri da manyan laifuka na rundunar da ya gudanar da cikakken bincike tare da gabatar da cikakken sakamakon kan wannan zargi.
Ya bayyana cewa duk da cewa lamarin da ake zargin ya faru ne a ranar 18 ga Maris, 2022, iyayen wacce ake tsare da ita ɗin sai kwanan nan su ka kawo rahoton.
Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a kammala binciken cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya ba da tabbacin cewa za a yi abinda ya dace, inda ya ƙara da cewa ko ɗin ko ko ma wanene a ka kama shi da laifi to za a hukunta shi yadda ya kamata,” in ji Ndukwe