
Tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya baiyana ɓacin ransa a kan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sakamakon rashin zuwa ya jajantawa al’ummar jihar kan ƙona matafiya 42 da ƴan ta’adda su ka yi.
A wata hira da BBC Hausa ta yi da shi a jiya Asabar, Bafarawa ya ce Buhari ya gaza magance rashin tsaro da ke addabar jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina.
Bafarawa ya baiyana cewa shugaba Buhari ba ya daraja rayukan al’ummar da su ka zaɓe shi.
“Abin da ya fi damu na shine yadda a ka maida rayukan al’umma basu da wata daraja. Ka duba rayukan da su ka salwanta a kwanaki 5 ko 6 da su ka gabata.
“An harbe mutane sannan a ka ƙone su a cikin mota amma Buhari ya tafi Legas bikin ƙaddamar da littafi, littafin da ba Kur’ani ko Bible ba.
“Bai zo Sokoto ya mana ta’aziya ba sai dai kawai ya turo wakilai.
“Lokacin da ya ke kamfen neman zaɓe ai da kansa ya zo, ba aikowa ya yi ba, sabo da ya na neman kuri’a.
“Me ya hana shi zuwa yai mana ta’aziya da jaje, amma ya tafi Legas wajen kaddamar da littafi? Mu dai kawai sai dai mu ce Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Sabon Birni, Shinkafi, Goronyo na cikin mawuyacin hali.
“Mu dai kawai sai dai mu ci gaba da addu’a a kan Allah Ya yaye mana Ya kuma kare mu,” in ji Bafarawa.