
Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar shugabancin Nijeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Attahiru Bafarawa ya yi jan kunne ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro kan abinda ya kira kisan kiyasi da fulani makiyaya ke yi akan al’ummar jihar Binuwe.
Bafarawa ya yi jan kunnen ne a lokacin da ya kai ta’aziyya ga gwamnan jihar Binuwe, Samuel Ortom, a garin Makurdi, babban birnin jihar ta Binuwe.
A lokacin da ya ke gabatar da jawabi, Bafarawa ya ce: “Jihar Binuwe jiha ce da ta samar da ‘ya’yan arewa na gari masu hangen nesa wadanda suka yi namijin kokari wajen hada kan arewa da sanya yankin akan turba, saboda haka babu wani dalili da zai sanya wasu mutane ko su wane ne su farma wannan al’umma da ta dade tana bayar da gudunmawa ga yankin arewa da ma kasa baki daya da kisa babu ji babu gani.
“To, wai me zai sa ma mu ci gaba da zancen yin zaben 2019 a kasar da babu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Babu wani muhimmin abu da za ka iya yi wa wata al’umma gata da ya fi samar musu da zaman lafiya. Sai an samar mana da zaman lafiya ne za iya zuwa mana da zancen zabe, don samar da zaman lafiya kamar samarwa rayuwa inda za ta zauna ne.”
Ya ci gaba da cewa, arewa ba za ta taba cika arewa ba a matsayinta na yanki ba tare da jihar Binuwe ba, saboda jihar Binuwe ta yi rawar gani wajen kafa harsashin gina arewa kuma gudunmawar da jihar ta baiwa arewa har gobe na da tasiri wajen ci gaba da kasancewar arewa
“Adu Ogbe da Sanata Barnabas Gemade sun rike matsayin shugabancin jam’iyyar PDP a lokacin da ita ke mulkin Nijeriya, kuma sun rike wannan matsayi ne a lokacin da damar shugabancin ya ke na ‘yan arewa. Wannan ya tabbatar da jiharsu a matsayin jihar arewa su kuma a matsayin ‘yan arewa.
“Wannan kashe-kashe da ya faru a wannan jihar, kashe-kashe ne da ko shakka na da alaka da siyasa, a saboda haka sai an yi amfani da hikimar siyasa wajen kawo karshen kashe-kashen ba wai kawai da karfin hukuma ba.
“Ko shakka babu, rikicin fulani makiya da monoma a fadin kasar nan lamari ne da ya zama ruwan dare gama duniya a fadin kasar nan, saboda haka babu wani dalili na nuna yatsa ga gwamnonin da abin ya faru a jiharsu ko ga shugaban kasa.
“Amma kuma wajibin gwamnatin tarayya ne da ta cire kasala wajen kawo karshen wannan kashe-kashe a jihar Binuwe da ma sauran jihohin kasar nan da ke fama da wannan rikici. A kokarin tabbatar da zaman lafiyar kasar nan, dole sai Shugaba Buhari sai ya sanya mutanen da ya dace ba tare da nuna bambancin siyasa ba,” a cewar Bafarawan.
Daga karshe, Bafarawa ya mika gudunmawar Naira miliyan goma ga wadanda abin ya shafa.
Gwamna Ortom, a nasa jawabin ya yi godiya ga Bafarawa bisa karamcin da ya nunawa mutanen jihar Binuwe.
Ortom ya ci gaba da cewa, Fulani makiyaya sun sauya daga yadda aka sansu a baya, yanzu sun dauki wani girman kai sun dorawa kansu kawai don gwamnati ta barsu suna yin abin da suka ga dama
A cedar gwamnan, ”Ko a jiya ma sai da fulani makiyaya suka kone gida mallakar tsohon baban jojin jiha, Augustine Utsaha tare da kashe rayuka da dama banda dukiyoyin al’umma da suka lalata duk a karamar hukuma Guma,” Gwamna Ortom ya koka.”