
Sanatan Filato ta Kudu, Farfesa Nora Ladi Dadu’ut ta samar da burtsatse da banɗakuna a wasu makarantu da ke mazaɓar ta.
Dadu’ut ta ƙaddamar da aiyukan a wasu zaɓaɓɓun makarantu a kewayen Ƙananan Hukumomi 6 na mazaɓar ta.
Yayin ƙaddamar da aiyukan, Sanatan ta ce ta aiwatar da su ne domin tana da sha’awar tsafta a guraren jama’a saboda ya hana hana lalacewar muhalli sannan ya na taimakawa karatun ƴan mata.
Dadu’ut, wacce ta ke farfesan harshen faransanci ta ƙara da cewa ta na da ra’ayin karatun yara tun su na ƙanana, inda ta ƙara da cewa hakan ne ma ya sanya ta gina ajujuwa a wasu makarantu ta kuma samar da kayaiyakin karatu .