Home Labarai Bahaya a sarari: An yankewa mutane 124 hukuncin aikin gaiya a Ogun

Bahaya a sarari: An yankewa mutane 124 hukuncin aikin gaiya a Ogun

0
Bahaya a sarari: An yankewa mutane 124 hukuncin aikin gaiya a Ogun

 

Sakamakon yin turoso a sarari, gwamnatin Jihar Ogun ta kama mutane 124, inda ba ta yi wata-wata ba ta yanke musu hukuncin yin aikin gaiya a cikin unguwanni.

Mai baiwa Gwamna Shawara kan Muhalli, Dapo Abiodun da kuma Shugaban Hukumar kula da Shara ta Jihar Ogun, Ola Oresanya ne su ka baiyana hakan ga manema labarai a jiya Alhamis a Abeokuta.

Sun ce an kama masu yin bahaya a sarari ne a gurare da dama a jihar, inda a ka kama 82 a Mowe-Ibafo, yankin Ƙaramar Hukumar Obafemi-Owode a jihar.

Oresanya ya gargaɗi direbobin manyan motoci da su dena yin bahaya a gefe da tsakiyar titi idan sun tsaya.

Ya yi kira gare su da su riƙa zuwa gidajen wanka da bahaya na kuɗi maimakon aikata wannan ta’ada mara amfani.

Ya baiyana cewa gwamnatin jihar ta baiwa gidajen mai da guraren sayar da abinci da su samar da banɗakuna a wani mataki na aikin al’umma.