
Sakataren kungiyar kiristoci ta kasa reshen jihar Kaduna Rabaran Sunday Ibrahim ya bayyana cewar bai kamata Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sassauta dokar hana fita ba a wasu yankunan jihar Kaduna kuma a tsaurarawa wasu ba.
A wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, Rabaran Sunday ya bayyana cewar har yanzu akwai fargaba da kuma tsoron daukar fansa a zukatan mutane da yawa, abinda yake jefa tsoro da firgici.
Rabaran yayi fatan samun dawwamammen Zaman lafiya mai dorawa a jihar Kaduna da na Najeriya baki daya.