Home Siyasa 2023: Baiwa wani takara idan ba Tinubu ba gagarumar matsala ce — Shettima

2023: Baiwa wani takara idan ba Tinubu ba gagarumar matsala ce — Shettima

0
2023: Baiwa wani takara idan ba Tinubu ba gagarumar matsala ce — Shettima

L

 

 

Tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, na da karfin da zai iya tabbatar wa jam’iyyar nasara a zaben 2023, yana mai gargadin cewa duk wani yunkuri na canja wani mataki a kan haka zai zama bala’i ga jam’iyar.

Shettima, wanda kuma shi ne Darakta-Janar na kamfen din Tinubu, ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana a wani shiri na yau da kullum na gidan talabijin ɗin TVC mai taken Journalists Hangout a jiya Juma’a.

Ya ce: “Idan jam’iyyarmu tana son lashe zaben 2023, to Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne amsa.”

“Daga cikin ƴan takararmu na shugabancin ƙasa, kuma ba ina nufin kaskanci ga kowa ba, Asiwaju shi ne dan takara daya tilo da ke da goge wa ta siyasa kuma ya ke da jama’a a ko ina a faɗin ƙasar nan tsayin daka da fadin kasar nan, wanda shine zai iya fita wa koma ya doke tsohon Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar saboda gogewar sa da kuma matsayinsa a ƙasa”.

Duk wani yunƙuri na dauko wani, duk da cewa jam’iyyar na da iko saboda muna cikin tsarin dimokraɗiyya, amma ina jin tsoron hakan zai zama bala’i ga jam’iyyar.”