Home Cinikayya Bambancin tunanin mai kudi da mai arziki – Bello Galadanchi

Bambancin tunanin mai kudi da mai arziki – Bello Galadanchi

0
Bambancin tunanin mai kudi da mai arziki – Bello Galadanchi
Bello Galadanchi
1.MAI KUDI NA RAYUWA NE A CIKIN WADATA  – MAI ARZIKI KUWA BASHI DA MATSALA WAJEN TAFIYAR DA RAYUWA A TAKURE
Tunanin mai kudi shine zama cikin wadata ne gimshikin farin ciki, shi kuwa mai arziki ya fahimci cewa saka kansa a cikin takura na bude idanunsa da bashi hikimomin warware matsalolin da zasu bashi damar kirkirar hanyoyi masu dorewa na samun kudade. Babu shakka fara sana’a jefa kaine a cikin takura da kasada, amma kuma sai da kasada ake bude kofofin alherin da ragowar jama’a suke tsoro da fargaba. Ka rungumi zama cikin takura. Akwai kalubale, amma farashin da zaka biya kennan domin cimma burinka na rayuwa.
Kayi watsi da zama cikin wadata, sannan ka nazarci ire-iren damammakin da kake su. Yin aiki a karkashin wani zai iya baka wadata, amma idan kana so kayi arziki, to dole sai ka shiga takura. Zaka iya faduwa, kuma wannan abu ne da zai kara maka hikima da hangen nesa. Idan baka fadi ba, to baka aiki tukuru.
2.MAI KUDI NA RAYUWA NE FIYE DA HALIN DA YAKE DA SHI – MAI ARZIKI KUWA A SAUKAKE YAKE RAYUWA
Zai yi wahala kaga mai arziki yana tuka motar miliyoyin nera irin wadda babu kamar ta a garin baki daya, ko ya zauna a katafaren gidan da duk garin babu irinsa. Masu arziki basa sayen kadarorin da darajarsu ke faduwa, sun fi mayar da hankali wajen mallakar kadarorin da darajarsu ke karuwa. Mafi yawancin masu arziki suna amfani da motoci ne wadanda basu da tsada sosai, kuma sukan dade basu canza ba. Ka tuna cewa idan kana samun Nera miliyan goma a shekara, sannan kana kashe Nera miliyan goma a kowace shekara, to baka da ko sisi. Babu abun sha’awa da mutuntawa kamar mutumin dake rayuwa dai-dai karfin da Allah Ya bashi.
3.YUNKURIN MAIKUDI SHINE YA SAMU KARIN MATSAYI A WAJEN AIKI – MAI ARZIKI KUWA SHINE YA MALLAKI WAJEN AIKIN
Mafi yawancin masu kudi suna aiki a karkashin wani ne. Suna da aikin yi, amma mafi yawancin masu arziki kuwa sun mallaki sana’o’in kansu ne. Masu arziki sun fahimci cewa suna bukatar mutane suyi aiki a karkashinsu domin dukiyar su ta karu. Masu arzikin duniya na mayar da hankali ne wajen kulla dangantaka, ragowar jama’a kuwa albashi suke nema.
4.MAI KUDI ABOKIN KOWA NE – MAI ARZIKI KUWA SAI YA ZABA
Masu arziki sun fahimci cewa idan suka zagaye kansu da matanen da suka yi nasara a rayuwa, to suma zasu yi nasara. Idan kuwa ka zagaye kanka da mutanen da zuciyar su ta mutu, to babu shakka zasu kashe maka zuciya. Arzikinka kusan daya yake da na abokan ka guda uku, saboda haka idan kana so ya karu, to ka fara muamala da mutanen da suka fi ka hali. Muhimmin abu shine ka fahimci yadda mutane masu nasara suke tunani. Idan kana so kayi arziki, to ka fara tunani kamar mutane masu arziki. Ka tabbatar kana share lokaci mai yawa tare da mutanen da suka fika nasara a rayuwa.
5.MAI KUDI NEMAN KUDI YAKE – MAI ARZIKI KUWA NEMAN ILIMI YAKE
Babu wuya mai kudi ya canza aiki ko sana’a idan har yaga inda zai samu karin kudi. Mai arziki ya fahimci cewa nufin aiki tukuru ba don neman kudi bane kawai, musamman a lokacin da yake da kuruciya. Wannan lokacin na neman ilimi ne da halaye, da hikimomin da zasu kaisu ga samun kudi. Mai arziki zai iya kama aiki a matsayin akawun shago domin fahimtar yadda duniyar saye da sayarwa take, ko kuma aiki a banki domin lakantar tsarin kudi da amfani da shi. Idan har kana so kayi arziki, to ka ringa aiki saboda neman ilimi da hikimomin da zasu sa kayi arziki. Albashi ba zai sa kayi arziki ba. Idan kana da kuruciya, to kayi ayyuka domin neman ilimi, ba don neman kudi ba.