
Gwamnan Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya kuma mai neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa ya ce yana jiran Shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi umarni tukunna game da janye takarar tasa.
Badaru na magana ne yayin wata hira da BBC Hausa jim kaɗan bayan gwamnonin Arewa 11 sun shawaraci Buhari ya zaɓi magajinsa daga ɓangaren kudancin ƙasar tare da shawartar ‘yan takarar Arewa a APC su janye.
“Ai ban isa na janye takara ba sai abin da baba Buhari ya ce,” kamar yadda gwamnan ya faɗa wa wakilin BBC Zahradden Lawan.
“Idan ya ce a yi takara a yi, idan kuma ya ce a mayar Kudu…za mu faɗa wa ‘yan Arawan su yi haƙuri baba ya ce Kudu.
“Kamar yadda ka gani a waccen takarda, idan wannan ce masalahar to na yarda da ita.”
Yayin ganawar da suka yi da Shugaba Buhari a daren jiya Asabar, gwamnonin sun faɗa wa shugaban cewa kishin ƙasa da kuma makomar APC ce ta sa suka ɗauki matakin, inda shi kuma ya umarci ‘yan takarar 23 su je su yi masalaha a tsakaninsu.