Home Labarai Ban taɓa nadamar zama ɗan sanda ba — CP Dikko

Ban taɓa nadamar zama ɗan sanda ba — CP Dikko

0
Ban taɓa nadamar zama ɗan sanda ba — CP Dikko

 

 

 

Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ce bai taɓa yin nadamar shiga aikin ɗan sanda ba a tsawon shekaru 35 da ya yi yana aikin.

CP Dikko ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano a lokacin da ya ke gabatar da laccar bankwana da ya yi a shelkwatar rundunar ƴan sanda da ke Bompai a yau Litinin.

Kwamishinan, wanda ya kai shekarun ritaya na aiki, ya shawarci ƴan sanda da su ci gaba da bin ƙa’idoji da dokokin aikin, inda ya kuma hore su da su guji shiga duk wani nau’i na cin+hanci da rashawa.

Dikko ya kuma yaba da goyon baya da haɗin kai da ya samu a lokacinsa daga manyan jami’an gudanarwa na rundunar ƴan sanda ta Kano, wanda a cewar sa, ya kai ga nasarar da aka samu ta fuskar tsaro a Kano.

CP Dikko ya buƙaci jami’an ‘yan sandan Najeriya da su kara himma da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Ya yaba da haɗin kan da ya samu tsakanin jami’an tsaro a Kano, yana mai jaddada cewa wannan shi ne sirrin zaman lafiya da aka samu a jihar Kano.

CP Sama’ila Dikko ya yaba da irin namijin kokarin da babban sufeton ‘yan sandan ya yi na ganin an inganta walwalar ‘yan sanda.