Home Labarai Ban taba karbar albashi a matsayin gwamna ba – Gwamna Aregbesola

Ban taba karbar albashi a matsayin gwamna ba – Gwamna Aregbesola

0
Ban taba karbar albashi a matsayin gwamna ba – Gwamna Aregbesola

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnan jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola ya yi ikirarin cewa ko sisin kobo bai karba a matsayin albashi ba tun da ya hau karagar gwamnan jiharsa ta Osun a shekarar 2010 kuma manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati da a turance a ke kira da permanent secretaries sun fi mataimakinsa daukar albashi.

Gwamna Aregbesola ya fadi hakan ne a yayin da ya ke zantawa da manema labarai da kuma al’ummar jihar  a karshen makon nan a wani shiri da aka yi wa lakabi da “Ogbeni Till Daybreak”, inda gwamnan ya baiwa al’umma da ‘yan jarida dama su yi masa tambayoyi game da gwamnatinsa.

Da aka tambaye shi game da yawan bashin da ake bin jihar, sai nan take ya umarci babban akanta na jihar, Mista Kolawole Akintayo da ya bada jimilar bashin da ake bin jihar.

Akintayo ya bayyana cewa zuwa yanzu dai ana bin jihar Osun Naira biliyan 143.6 ne bayan da jihar ta biya Naira biliyan 28 daga cikin Naira biliyan 171.4 da ake bin ta.

Aregbesola ya tabbatar da cewa jihar za ta biya dukkan basussukan da ake bin ta a shekarar 2019 inda bashin SUKUK kuma da adadinsa ya kai Naira biliyan 11.4, jihar za ta biya a shekarar 2020.

Gwamna Aregbesola ya bayyana dalilin da ya sanya gwamnati bata karbar bashi don sanya hannun jari a wata harka ta kasuwanci sai don ta yi ayyukan raya kasa shi ne saboda a tsarin yadda gwamnatoci ke tafiya a Nijeriya shi ne gwamnati ba ‘yar kasuwa bace, sai dai tana samar da yanayi mai kyau don gudanar da kasuwanci ga ‘yan kasuwa.