
Fasto Enoch Adeboye, Janar mai kula da Cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG, ya ce bai taɓa yin kira ga Kiristoci da su sayi bindigogi don kare kansu ba.
“Ban taɓa cewa Kiristoci su je su sayi bindigogi ba. Samson, a cikin Littafi Mai-Tsarki bai yi faɗa da bindigogi ba, ”
Fitaccen malamin ya faɗi hakan ne a yau Lahadi a wani shirin talabijin na kai tsaye na godiya na wata-wata na cocin.
Bayanin ya zo ne a kan rahotannin kafofin watsa labarai cewa Faston ya ce yanzu “wuta-da-wuta” ce ga duk wani hari da aka kai wa Kiristoci.
“Kada ku sayi bindigogi. Ku dama kisa ba halinku ba ne. Dole ne mu tabbatar cewa shaiɗanu ba su zo cocinmu ba, don haka kar ku je ku sayi bindigogi,’’ inji shi.
A ranar 2 ga watan Yuli ne dai Fasto Adeboye ya bukaci mabiya cocin da kada su ji tsoron halartar cocin saboda harin da ‘yan ta’adda suka kai a coci a garin Owo na jihar Ondo.