
Ɗan takarar kujerar Sanata a Kano ta Tsakiya, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa ya ce zai yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Mallam Ibrahim Shekarau ritaya a siyasa a 2023.
Rahotanni da su ke fitowa a jiya Litinin sun baiyana cewa Zaura, wanda a ka fi sani da AA Zaura, ya yi hira da wasu ƴan jaridu a Kano, inda ya ce yana da yakinin zai lashe zaɓen Kano ta Tsakiya a 2023, kuma hakan zai sanya ya yi wa tsofaffin gwamnonin biyu, Kwankwaso da Shekarau ritaya irin ta siyasa.
Sai dai kuma, a wani martani na gaggawa, Zaura a wata sanarwar sanya fitar, ya ce shi bai faɗi hakan ba.
Ya ce, “An jawo hankali na kan wasu wallafe -wallafe da ke zagayawa yanzu haka a jaridun yanar gizo gizo, inda ake ikirarin nace, “zan yi wa Kwankwaso da Shekarau ritaya”. Gaskiyar Magana itace babu inda na ce haka, hasalima na kirasu da iyayena a cikin hirar da aka dakko zancen.
“Abinda nace a lokacin da ƴan jaridu su ka tambayeni:” Ya ya ka ke ganin F’fuskantar manyan jiga jigai guda 2, tsofaffin G’gwamnoni, sanatoci kuma tsoffin ministoci a wannan zabe na shekarar 2023?
“Abinda nace shine, ” da yaddar Allah, ni zan lashe zaɓen na 2023, idan Allah ya bani, kaga sai Malam ibrahim Shekarau da Sanata Rabi’u Musa kwankwaso su je su huta. Dukan su sun yi aiki tukuru a lokutansu, kuma idan ka duba, zaka ga sad’nda suka yi wannan kokarin suna da jini a jika, saboda haka wadannan iyayen nawa guda biyu zasuje su huta insha ALLAH a shekarar 2023.
Inaso al’umma su sani cewa ban taba aibanta ko cin zarafin, ko da sa’a na ba, balle wanda na ke K’kallo a sa’oin iyayena, kuma na ke kallonsu a iyaye. Ban taɓa ɗaukar siyasa a ɓatanci ba, kuma ban yarda da siyasar cin zarafi, mutunci da ɓatanci ba. Mu na siyasa ne ta muntuntawa da karramawa don cigaba.
“Ina kira ga gidajen jaridun da su ke yaɗa wannan irin labaran ƙanzon kurege da su guji ayi amfani da su don cimma burin siyasa ganin cewa hakan na da illa hatta a shari’ance,” in ji Zaura.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa AA Zaura dai zai fafata da Shekarau a zaɓen Kano ta Tsakiya a 2023, bayan ya fice da ga jam’iyar APC zuwa NNPP.