Home Labarai 2027: Bana shirin zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga kowa — Obi

2027: Bana shirin zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga kowa — Obi

0
2027: Bana shirin zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga kowa — Obi

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party a zaben 2027, Peter Obi, ya ce bashi da sha’awar zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga kowa a zaben 2027.

Daily Trust ta rawaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a yau Asabar a shafin sa na X.

Acewarsa, an yi wa wasu kalamai da ya yi yayin ganawa da News Central TV gurguwar fahimta.

Obi ya ce a yayin tattaunawar, ya yi amfani da damar wajen yin bayani kan matsayar sa dalla-dalla, amma wasu mutanen suka dinga yada akasin hakan.

“Domin kaucewa rudani, ni ban ce zan zama mataimakin shugaban kasa ba”.

” Na sha fada cewa, a shirye nake nayi aiki da wadanda ke son gina sabuwar Nijeriya.

“Bana son zama irin mutanen dake ta babatu kan batun 2027 a yayin da ‘yan Nijeriya ke fama da yunwa da matsalar tsaro da sauran kalubale”, inji Obi.