
Irin kungiyoyin nan ne na turawa suka zo nan Kano zasu yi bincike domin samar da ruwan sha a wasu gurare ta hanyar haka musu rijiyoyi ,sai suka kirawo yan uwanmu yan boko da suka tara digiririka a fannin labarin kasa (amma ba fa ina nufin tara digirrika bashi da amfani ba, domin ina da guda biyu) Suka zo suka kawo musu tarin takaddu na irin binciken nan da suka yi aka fara musayar turanci ko ta ina ,da aka yi nisa sai turawan nan suka ce to kafin a aiwatar da aikin da Allah a nemo musu mai hakar rijiya,
Sai aka tafi can asalin karamar hukumar mu ta Gezawa aka samo wani Baba mai hakar rijiya wanda ya dade yana yi,aka kawo shi gaban turawannan ,Baba yana karkarwa suka ce masa kada ya damu ,aka samu tafinta ,Turawan nan suka fara tambayar Dattijon nan ,da Baba mai hakar rijiya ya fara zuba ana fassarawa ,yace kasa kaza dake gari kaza tana da siffa kaza,wannan tana iya samar da ruwan dadi,wata kuma ta zartsi,sannan Dattijo mai hakar Rijiya saboda shekaru da ya diba yanayi yace wa Turawannan gari kaza ko alkarya kaza kasarsu mai kama kaza baza ta iya bayar da ruwa ba,
Turawannan bayan sun gama jin bahasin Baba mai hakar Rijiya sai suka je suka aiwatar da samar da ruwan sha game da abinda ya gaya musu, bayan an kammala aka kirawo Baba mai hakar Rijiya na karamar hukumar mu ta Gezawa aka shaka masa Daloli ,Baba mai hakar Rijya ya tafi yana nishadi, kwarewa ta yi aiki .
Baba ya dade yana hakar Rijiya ga kuma abinda ya yi sanadin samarwa.