
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rade radin da ake yadawa cewa yana cikin yunkurin zargin da ake yi na tsige Muhammadu Sanusi na II daga matsayin Sarkin Kano.
Leadership ta rawaito cewa Ganduje ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan fannin yada labarai da wayar da kan al’umma, Chief Oliver Okpala ya fitar.
Shugaban na APC na mayar da martani ne kan wani rahoto dake yawo a shafukan sada zumunta mai taken “Ganduje na jagorantar sabon yunkuri na tsige Sarki Muhammad Sanusi a matsayin Sarkin Kano”.
Rahotan ya ambato cewa “Majiyoyi daga fadar Kofar Kudu sun ce, Ganduje da wasu manyan mutane na yunkurin cire tsohon Gwamnan Bankin CBN a matsayin Sarkin Kano na 16 kuma shugaban majalisar Sarakunan Kano”.
Sai dai a martanin da ya mayar Ganduje ya ce babu gaskiya a zargin, inda ya jaddada cewa bashi da hannu a yunkurin tsige Sarki Sanusi.
Tsohon Gwamnan, ya ce shi yanzu ba Gwamna bane kuma ba shugaban majalisa ba don haka bashi da hannu kan tsigewa ko nada Sarki a Kano.