
Bankin Jaiz ya naɗa Dakta Sirajo Salisu a matsayin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa, kamar yadda Sakataren Kamfani, Mohammed Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwa a Legas a jiya Litinin.
Shehu, a cikin sanarwar da ya mika wa Kamfanin Hada-hadar Canjin Kuɗaɗe na na Najeriya, NGX, ya ce nadin zai fara aiki ne daga ranar 16 ga watan Oktoba.
Salisun, shi ne zai maye gurbin Manajan Darakta mai ci, Hassan.
Har zuwa lokacin da aka nada shi, Mista Salisu ya kasance Babban Darakta na Ci gaban Kasuwanci, shiyyar Arewa.
Shi ne Sahihin Jami’in Magance Matsalar Kasuwanci, CRM a cibiyar bada lamuni , FICA, kuma babban manaja, a cibiyar horas da ma’aikatan banki ta ƙasa , CIBN.
Ya fara aikin banki ne a 1992 tare da bankin Inland Plc a matsayin mai kula da harkokin banki, ya kuma kai matsayin babban manaja a 2009 da First Inland Bank Plc.