Home Kasuwanci Bankin Jaiz zai sake gina kasuwar terminus ta Jos kyauta — PICTDA

Bankin Jaiz zai sake gina kasuwar terminus ta Jos kyauta — PICTDA

0
Bankin Jaiz zai sake gina kasuwar terminus ta Jos kyauta — PICTDA

 

David Daser, Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Jihar Filato, PICTDA, ya bayyana cewa bankin Jaiz zai sake gina babbar kasuwar Jos, mai suna terminus, ba tare da gwamnati biya kudi ba.

An lalata babbar kasuwar ta Jos, ɗaya daga cikin mafi girma a yammacin Afirka, a lokacin rikicin Jos na 2001, kuma tun lokacin an yi watsi da ita.

Da ya ke magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Alhamis a Jos, Daser ya ce gwamnati mai ci ta ɗauki gaɓaran sake gina kasuwar, shine sai ta tuntubi bankin Jaiz domin ya yi aikin.

“A cikin shekaru bakwai da suka gabata, yawancin bankunan kasuwanci, masu zuba jari masu zaman kansu da ma wasu kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun nuna sha’awar aikin.

“har sai da ta kai ga an baiwa wani fitaccen dan Jihar Plateau aikin, dalilin da ya sa aka fara ruguje kasuwar domin sake gina ta, sai gashi ko sake Binta kan aikin ma bai yi ba.

“kwatsama sai ga bankin Jaiz ya nuna bukatar yin aikin ba tare da ko sisin gwamnati ko rance ba za a sake gina mana kasuwar mu ta terminus.

“Ba wai kawai nuna bukatar yin aikin na, a watan Agusta bankin zai fara ma aikin,” in ji shi.