
Sabon Alkalin Alkalan Najeriya, CJN, Olukayode Ariwoola, ya gargadi bangaren shari’a da su bar siyasa ga ƴan siyasa, kada su rika shiga harkokin su.
Ya kuma gargadi ƴan siyasa da su daina tsoma baki a harkokin shari’a a yayin da zaben 2023 ke gabato wa.
Ariwoola ya bayyana hakan ne yayin wata liyafar da gwamnatin jihar Oyo ta shirya masa a ranar Lahadi.
CJN ya ce: “A shirye muke kuma muna jira kuma ba za mu baiwa ƴan Najeriya kunya ba. Ƴan siyasa su bar shiga harkokin bangaren Shari’a domin a bar mu mu yi aikin mu
“Su yi abinsu, mu yi namu. Doka ba aba ce tsayayayya ba; abin da muke amfani da shi shine doka kamar yadda aka kafa ta. Mun nemi a yi wa kundin tsarin mulkin mu kwaskwarima akai-akai.
“Akwai batutuwa da dama da bai kamata su kai ga kotun koli ba a 2022. Da yawa dai al’amuran cikin gida ne na jam’iyyun siyasa. Me ya sa muka kawo haka a kotu domin mu yanke hukunci alhali tsarin mulkin ku ya nuna muku hanya?
“Bi hanya. Kuma tsarin mulkin jam’iyya ya kasance kasa da kundin tsarin mulkin Najeriya. Don haka duk inda aka samu rikici to kundin tsarin mulkin Nijeriya ya yi tasiri.
“Don haka muna jira, muna addu’a sosai, Allah Ya taimake mu, kasar nan ba za ta rabu ba, kasar nan ba za ta ruguje a zamaninmu da lokacinku ba. Mun yi alƙawarin za mu yi iya ƙoƙarinmu ba tare da ɓata lokaci ba, kuma ba za mu ƙyale ku ba, ba za mu yi kasa a gwiwa ba ga ƴan Nijeriya.”
A nasa jawabin, gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce gwamnatinsa ta samar da yanayin da bangaren shari’a na gwamnati zai iya gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su, domin ta gane cewa shi ne ginshiki kuma gata ga talaka.