Home Labarai Bara: Gwamnatin Kano ta kama mabarata sama da 300

Bara: Gwamnatin Kano ta kama mabarata sama da 300

0
Bara: Gwamnatin Kano ta kama mabarata sama da 300

 

 

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kama almajirai sama da 300 maza da mata yara da manya a birnin jihar.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Shugaban Hukumar Hana Barace-barace ta Jihar Kano, Malam Albakari Mika’il ya ce mafi yawan waɗanda a ka kama ba almajirai bane da suke zuwa makaranta.

Albakari ya ce gwamnati ba za ta saurarawa duk wanda ta kama sau biyu ba, in da ya ce za ta miƙa su ga kotu domin ta yanke musu hukunci kamar yadda ya dace.

A cewar Mika’il, hukumar za ta mayar da wasu yaran gaban iyayensu, wasu kuma, musamman waɗanda a ka same su su na shaye-shaye, za a miƙa su ga Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA, da kuma miƙa wasun su ga rundunar Ƴan Sanda.

Malam Mika’il ya ƙara jaddada cewa za su cigaba da kamen almajirai da masu gararanba a kwaryar birnin Kano da kewaye domin tsaftace jihar da ga mabarata.

Wasu daga cikin almajiran da aka kama sun shaidawa manema labarai cewa an kama su ne da misalin karfe 3 na dare a unguwannin Sabongari, Tarauni titin IBB da sauransu.

Da yawansu sun ce sun yi nadama tare da bada tabbacin ba za su cigaba da gararanba a gari ba.