
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dauki dan wasan Wolves aro zuwa nan da karshen kakar wasanni ta ba.
Kungiyar za ta rika biyan dan wasan kudade sannan kuma a yarjejeniyar da aka cimma za ta iya sayan shi a a lokacin bazara.
Watanni 18 ne suka ragewa Traore a kungiyarsa ta Wolves kuma babu wata yarjejeniya a kasa ta neman ya tsawaita kwantaraginsa da kungiyar.
“Kowa ya san Barcelona kungiya ce da take cikin ran Adama. wannan komawar da zai yi cikar burinsa ne,” in ji shugaban bayar da atisaye na Wolves Scott Sellars
Traore ya fara kwallonsa ne a Barcelona gabanin ya koma Aston Villa a 2015.
Ya kuma shafe shekara biyu a kungiyar kafin daga bisani ya koma Wolves a 2018.