
Bayan shekara ɗaya da rabuwar sa da tsohuwar matarsa, basarake Ooni of Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, a ranar Talata yayi sabon aure, inda ya aure Mariam Anako, a matsayin sabuwar matar sa.
Anyi shagalin bikin auren ne a fadar sa dake Ile-Ife, a ciki jihar Osun.
A wani fefen video da mai maganada yawun basaraken ya wallafashi a shafin sa na sada zumunta Facebook, ya bayyana yace akasha shagalin bikin, cikin nishade da walwala.
Hakan dai na zuwane bayan basaraken sunyi baran baran da tsohuwar matar sa, kimanin watanni goma da suka wuce.