Home Labarai Bashir Gwandu abokin Yusuf Buhari da suka yi haɗari tare yana cikin ɗimuwa

Bashir Gwandu abokin Yusuf Buhari da suka yi haɗari tare yana cikin ɗimuwa

0
Bashir Gwandu abokin Yusuf Buhari da suka yi haɗari tare yana cikin ɗimuwa
Bashir Gwandu

Bashir gwandu babban aminin Yusuf Buhari da suka yi hadari tare, wanda yake cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai shima yana cikin halin dimuwa a a Asibitin Cerdarcest dake babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu tabbaci.

Bashir Gwandu dais hi ne babban abokin Yusuf Buhari kuma tare suka yi wannan mummunan hadari, amma bayanai sun nuna cewar shi bat a shi ake ba, duk kokarin da ake yi kan Yusuf Buhari ne.

Majiya mai tsuhe ta tabbatarwa da DAILY NIGERIAN HAUSA cewar, asali hadarin ya auku ne a lokacin das hi Yusuf Buhari ya kure malejin babur dinsa domin yaga ya cimma abokin tserensa Bashir Gwandu, a lokacin day a kure malejin ne suka yi taho mu gama, inda kowannensu yaji mummunan ciwo.

“Sun fadi yashe akan kwalta, kafin umarni yazo na a dauke su zuwa wani asibiti mafi kusa domin basu kulawar gaggawa.”

DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu tabbacin cewar, a lokacin da hadarin ya auku, akwai motar jami’an tsaro da take tare das u Yusuf Buhari take basu kariya a yayin da suka fito yin tseren a tsakaninsu akan titin Ahmadu Bello kusa kantin sayayya na NEXT a babban birnin tarayya.

Sai dai da safiyar Alhamis aka samu wata majiya mara tushe wadda tace an garzaya da Yusuf Buhari zuwa kasar Jamus domin cigaba da jinyarsa acan. Amma daga bisani Garba Shehu mai Magana da yawun Shugaban kasa yace wannan batu jita jita ne dab a shi da tushe balle makama.

Amma duk da haka, wata majiya mai tushe ta shaidawa DNH cewar, akwai yuwuwar fitar da Yusuf Buhari zuwa kasar waje daga zarar ya dan farfado.

Har ya zuwa yanzu, babu tabbas ko za’a fitar da Yusuf Buhari kasar waje tare da abokin hadarinsa Bashir Gwandu.