Home Labarai Bashir El-Rufai ga Shehu Sani: Da ni za ka yi, mahaifi na ya fi ƙarfin ka

Bashir El-Rufai ga Shehu Sani: Da ni za ka yi, mahaifi na ya fi ƙarfin ka

0
Bashir El-Rufai ga Shehu Sani: Da ni za ka yi, mahaifi na ya fi ƙarfin ka

Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna rashin jin daɗin sa ga sukar da Shehu Sani, tsohon Sanata Kaduna ta Tsakiya ke yi wa mahaifinsa.

Shehu Sani, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta kalubalanci tsohon gwamna El-Rufai da ya bayyana kadarorinsa daga shekarar da ya hau mulki, 2015 zuwa 2023.

Shehu Sani ya kuma zargi El-Rufai da tarawa jihar Kaduna ɗumbin bashi amma kuma ya na iƙirarin cewa bai taɓa satar ko kwabo a asusun jihar ba.

Hakazalika Shehu Sani ya ce El-Rufai na neman Bola Tinubu ya bashi muƙami, inda ya ce in ya isa ya bayyana abinda ke kunshe a fom din bayyana ƙarara da ya kai kotun bayyana kasar jami’an gwamnati.

Da ya ke maida martani, Bashir ya ce Shehu Sani ya dawo da yakin da ta ke ta twitter ga su sa’annin sa ba wai mahaifinsa ba.

Bashir ya ce Shehu Sani ya yi da shi domin El-Rufai ya fi ƙarfin sa.