
Daga Ubaidullahi Yahaya Kaura
Wata kotun shari’ar musulunci dake gudanar da zamanta a garin Gusau wadda mai shari’a Alhaji Muhammad ST. Shinkafi yake shugabanta, ta tura shugaban majalisar karamar Hukumar mulki ta Gusau Hon. Ibrahim Tanko da kansilan karamar Hukumar mai wakiltar mazabar Sabon Gari Hon. Ashiru Musa Nagari da kuma shugaban jam’iyyar APC na mazabar Sabongarin Gusau Mainasara Yahaya gidan yari.
Kotun ta tura wadannan mutanen ne zuwa gidan yari a sanadiyar zargin da ake yi masu da hannu wajen kada al-kur’ani mai girma cikin bandaki.
Bayan da aka karanta masu zargin da ake yi yimasu a gaban kotun, dukkan wadanda ake zargin sun musunta wannann zargin.
Daga nan sai mai shari’a Muhammad ST. Shinkafi ya bada sanarwar daga sauraron wannan kara da Gwamnatin jihar Zamfara ke yi da shugaban karamar Hukumar mulki ta Gusau da sauran wasu jama’a zuwa ranar Litinin 26/2/2018.