
Fitaccen Malamin addinin Islama a jihar Kano Sheikh Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo ya bayani kam mallakar birnin Ƙudus. A cewar Malamin, asali Musulmi da hakkin mallakar birnin Ƙudus, ya yi banin tarihin kafuwar birnin tun shekaru 3000 kafin haihuwar Annabi isah.
“Asalin birnin Ƙudus wasu larabawan kauye ne da ake kira kan’aniyyun suka kafa birnin, kuma mutanan suna magana da harshen larabci, “tsohon harshen larabci”. An yi yaki da larabawa kan wannan birni”
“Shekaru 2000 kafin haihuwar Annabi Isah, Annabi Ibrahim yayi hijira zuwa wannan yanki tare da matarsa Sarah a wannan yanki da ake kira Falastinu. Wadda matar Annabi Ibrahim ta haifi Ishaq, wanda shi kuma ya haifi Yakub, wanda tsatsonsa ke tukewa zuwa ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam”
“”Annabi Ibrahim da dan Ismail shi ne ya gina Masallacin Ƙudus mai alfarma, wanda shi ne masallaci na uku mafi daraja a wajen Musulmi. Annabi Ibrahim ya zabi birnin Kudus ya zama cibiyar mulki a wancan lokacin”.
Malamin yayi bayani mai tsawo daga alkurani da hadisi, inda ya kawo tarihin Annabawan Musulnci da suka zauna a wannan birni tundaga Annabi Ibrahim da sauran Annabawa da dama, dan haka Kasar Falastinu, kasa ce mai daraja a wajen Musulmi.
An taba baiwa Yahudawa damar kafa kasarsu a shekarar 1917, inda Ministan harkokin wajen Burtaniya na lokacin ya basu damar kafa kasarsu, inda yanzu Trump ya sake maimaita wancan umarni shekaru 100 bayan wancan umarni da aka basu.
An kafa kasar Israela ne a shekarar 1948, inda tun a wancan lokacin ne ta dinga fadada kan iyakokinta da kasashen da ke makwabtaka da ita musamman yankin gabar yamma da kogin Jordan da sauran sassa da suka hada da birnin Sina’a da sauran yankunan Sham.
Abinda Trump yayi sabawa abinda majalisar dinkin duniya ta yi yarjejeniya akansa. Don haka, abinda Trump yayi a yanzu ba zai taba canza tarihi ba, domin asali Yahudawa ba su da asali akan Ƙudus. A cewar Dakta Sani Riiyar Lemo.