Home Labarai Bauchi: Wani mutum ya kashe abokinsa saboda ya ki saya masa giya

Bauchi: Wani mutum ya kashe abokinsa saboda ya ki saya masa giya

0
Bauchi: Wani mutum ya kashe abokinsa saboda ya ki saya masa giya

Wani mutum a jihar Bauchi ya kashe babban abokinsa saboda ya ki saya masa giya a jihar Bauchi

Wanda ake zargin, Monday Ajasco, mai shekaru 29, dan garin Kafin Tafawa, yanzu haka yana hannun ‘yan sanda, ya kashe Abdularazak Ibrahim, mai shekaru 30, a wani gidan giya da ke Bagel a Ƙaramar Hukumar Dass.

‘Yan sandan sun ce mutanen biyu sun shiga zazzafar taƙaddama ne bayan da Ibrahim ya ki amincewa da ya saya wa Ajasco barasa a ranar Litinin da ta gabata.

Bayan wani lokaci, kamar yadda rahotanni su ka bayyana, sai dukkansu suka yanke shawarar barin dakin giyar suka tafi gidajensu.

A cewar wani ganau, ya ji Ibrahim yana kururuwa, yana isa wurin, ya same shi kwance a cikin jini, a daidai lokacin da Ajasco ke tsaye kusa da wanda abin ya shafa rike da kahon dabba a hannunsa.

Shaidar ya ce a hakan ya faru ne bayan da Ajasco ya fusata ya kuma yi barazanar daɓawa shaidar, wanda kuma abokin marigayin ne, lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya kashe abokin nasa.

‘Yan sandan sun ce a ranar Litinin din da ta gabata an daba wa Ibrahim wuka a wuya da wani abu mai kaifi da ake zargin kahon dabba ne.

Ya rasu ne a babban asibitin Dass.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu.