
Daruruwan ƴan Nijeriya ne yanzu haka suke binciko wasu wuraren yin bulaguro bayan da birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya kafa dokar hana su biza baki daya a watan Oktoba.
Daily Trust ta ruwaito a yau Asabar cewa, kafin dakatar da ƴan kasuwa a Nijeriya, Dubai ta fara tsaurara sharuddan biza ga masu neman izinin shiga da ga Nijeriya.
A halin yanzu dai, ƴan Najeriya da ke da fasfo din diflomasiyya da wasu kalilan ne ke samun damar shiga Dubai.
Har yanzu Dubai ta kasance wurin da ‘yan Najeriya da yawa suka zaba don dalilai da yawa, ciki har da kasuwanci, ilimi, shakatawa da yawon bude ido.
Sai dai bayan haramcin bizar, yanzu haka ‘yan Nijeriya da dama na yin balaguro zuwa kasashen Masar, Morocco da sauran kasashe.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga UAE kan dalilin dakatarwar, wasu na bada dalilin da munanan halayyar da wasu ɓatagarin ƴan Nijeriya ke nuna wa a Dubai.
Kafin dakatarwar dai an samu rahotanni da dama kan yadda ake kama wasu ƴan Nijeriya a UAE bisa zargin sata da aikata laifuka ta yanar gizo. Wasu an yi musu shari’a an daure su, yayin da wasu kuma a ka auno su zuwa gida.