Home Siyasa Bayan ya fice daga APC, Injiniya Bashir ya samu takarar gwamnan Kano a jam’iyar LP

Bayan ya fice daga APC, Injiniya Bashir ya samu takarar gwamnan Kano a jam’iyar LP

0
Bayan ya fice daga APC, Injiniya Bashir ya samu takarar gwamnan Kano a jam’iyar LP

 

Tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyar APC a jihar Kano, Injiniya Bashir I. Bashir, ya samu takara a jam’iyar Labour Party, LP, kwanaki kaɗan bayan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyar.

A wata hira ta musamman da Daily Nigerian Hausa a jiya Juma’a, Injiniya Bashir ya ce ya bar APC ne saboda rashin adalci da kuma karya tsarin dimokuraɗiyya.

A cewar sa, ko da ya bar APC, ya yi yunƙurin koma wa jam’iyar NNPP mai kayan marmari, inda ya ce da ya je can ma sai ya fahimci duk kanwar ja ce.

Ya ce shi ɗan siyasa ne gogagge kuma mai son ci gaba, inda ya ƙara da cewa gogewarsa da da ƙwarewarsa ce ta sa ya ke da burin ya mulki Kano domin ya fitar da ita daga mawuyacin halin da ta ke ciki.

Injiniya Bashir ya bayyana cewa bayan ficewar sa daga APC, tuni shugabancin jam’iyar LP da kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar, Peter Obi su ka gayyace shi wani zama a Abuja.

Ya ƙara da cewa “da mu ka yi zaman, sai mu ka ji manufofin su da tsare-tsaren su sun yi dai-dai da irin wanda mu ke so mu kawo a jihar Kano.

“Sun nuna mana manufofinsu na samar da tsaro, gyara tattalin arziki, ilimi, lafiya, wutar lantarki, bunƙasa harkokin noma da sauransu, sai mu ka ga ainihin tsarin da mu ke da shi kenan, saboda haka sai muka amince mu ka shiga jam’iyar, Injiniya Bashir.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su riƙa zaɓar mutane da su ke nagartattu ba wai jam’iya ba, inda ya nuna ƙwarin gwiwa cewa zai lashe zaɓen kuma zai ciyar da Kano gaba idan ya ci zaɓen.