
A ƙalla mutane 97 ne su ka shaƙi iskar ƴanci bayan da ƴan fashin daji su ka sake su sakamakon luguden wuta ta sama da sojojin Nijeriya su ke yi a kwanakin nan a dajikan Shinkafi da Tsafe.
Duk da cewa ƴan sanda sun ce su ne su ka kuɓutar da mutanen, wasu majiyoyi sun ce ƴan fashin dajin ne su ka sako su domin su nuna cewa a shirye su ke da a yi sulhu bayan hare-haren da sojoji ke Kai musu.
Kwamishinan Ƴan Sanda, Ayuba Elkanna ne ya baiyana hakan a taron manema labarai a jiya Talata a Gusau.
Elkanna ya ce sakin mutanen ya biyo bayan luguden wuta da sojoji ke kaiwa sansanin ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji, wanda ya ke aikata laifukan sa a Ƙananan Hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji.
A tuna cewa a ranar 3 ga watan Janairu, ƴan sanda da ke yin sintiri na musamman a Shinkafi sun samu bayanin sirri cewa an hango wasu mutane da a ka yi garkuwa da su, an sake su amma sun rasa inda za su je.
Sai ƴan-sandan ba su yi ƙasa a gwiwa ba, inda su ka haɗa kai da tubabbun ƴan ta’addan da kuma ƴan kato da gora su ka shiga jejin har su ka kuɓutar da mutane 68.
Inda ya ƙara da cewa mutane sun shafe watanni uku a hannun ƴan fashin daji, In da su ka haɗa da maza manya 33, yara maza 7, yara mata 3, da kuma mata 25 da suka haɗa da masu ciki da kuma masu shayarwa.