Home Siyasa Bayan ya sauya sheƙa zuwa APC, gwamna Matawalle na yunƙurin rushe sakateriyar PDP a Zamfara

Bayan ya sauya sheƙa zuwa APC, gwamna Matawalle na yunƙurin rushe sakateriyar PDP a Zamfara

0
Bayan ya sauya sheƙa zuwa APC, gwamna Matawalle na yunƙurin rushe sakateriyar PDP a Zamfara

 

 

Watanni 5 kacal da sauya sheƙa da ga jami’yar PDP zuwa ta APC, gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi wa sakateriyar PDP ɗin sheda domin rushe ta.

Tuni dai PDP ɗin ta baiyana cewa ta shigar da ƙara a kotu, inda ta ke ƙalubalantar Hukumar kula da Tsarin Gari da Gine-gine ta Zamfara, ZUREP, kan shaidar da ta yi wa sakateriyar jam’iyar domin rushewa.

Shugaban jam’iyar PDP na riƙo a jihar, Bala Mande, shi ne ya shaidawa manema labarai bayan wata ganawa ta gaggawa da shugabannin jam’iyar su ka yi a ranar Laraba.

Shi dai Mande shine Shugaban Ma’aikatan Fadar gwamna Matawalle ne a lokacin ya na PDP amma ya ci gaba da zamansa a jam’iyar bayan da gwamnan ya sauya sheƙa zuwa APC a ranar 27 ga watan Yuni.

A cewar Mande, shaidar da a ka yiwa sakateriyar PDP ɗin wani yunƙuri ne na bita-da-ƙulli da kuma yi wa ƴan jam’iya da shugabanninta barazana.

“Mu dai ƴan jam’iyar PDP mutane ne ma su bin doka kuma tuni mu ka garzaya kotu domin a bi mana haƙƙinmu,”

Mande, wanda kanal ɗin sojoji ne mai murabus, ya kira ƴan jam’iya da su zama ma su bin doka da oda, kuma ka da su ɗauki doka a hannunsu.

A ƙarar da PDP ɗin ta shigar a babbar kotun jihar da ke Gusau, ta nemi kotun da ta yi fatali da sanarwar da ZUREP ta fitar ta rushe sakateriyar a ranar 29 ga watan Oktoba ta kuma aiyana ta a matsayin haramtacciya.

Sannan PDP ta nemi kotun da ta tilastawa ZUREP ɗin ta biya ta Naira miliyan 60.