Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Fati Muhammad ta dawo Kannywood, bayan shafe shekaru goma sha huɗu da daina sana’ar.
Dawowar Fati ta kasance tare da fatan alheri daga masoyanta da masoyan fina-finan Hausa.
Ta dawo ne a matsayin mai shirya fina-finai, kamar yadda wata gajeriyar sanarwa ta bayyana a shafin Facebook na ‘Kannywoodcelebrities’.
A ranar Talatar nan dai sabbin hotunan jarumar su ka karaɗe shafukan Sada Zumunta, musamman Facebook da instagram, wanda hakan ke nuni da cewa al’umma suna farin ciki da dawowarta harkar fina-finan Hausa.
A cikin hotunan, a kwai wanda a ka nuno Fatin a zaune kan wata kujera yayin da ake ɗaukar wani sabon fim, wanda za ta taka rawa a cikin sa.
A na tunanin cewa wannan shine shiri na farko bayan dawowarta harkar fina-finan Hausa.
Fati, ƴar asalin Jihar Adamawa, ta fara harkar fim tun tana ƙarama.
Fina-finan ta da su ka yi fice sun hada da Sangaya, Zarge, Marainiya, Mujadala, Kudiri, Tutar So, Garwashi, Tawakkali, Gasa, Abadan Da’iman, Zo mu Zauna, Tangarda, Hujja, Al’ajabi, Halacci, Samodara, Zumunci, Murmushin Alkawari, Gimbiya, Bakandamiya, Taskar Rayuwa, Babban Gari da dai sauransu.