Home Labarai Bayan sumamen SSS, Emefiele ya dawo bakin aiki

Bayan sumamen SSS, Emefiele ya dawo bakin aiki

0
Bayan sumamen SSS, Emefiele ya dawo bakin aiki

Gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele ya koma bakin aikinsa bayan hutun da ya ke yi a kasar waje, kamar yadda wata sanarwa daga bankin ta bayyana.

Tun da fari, DAILY NIGERIAN ta rawaito yadda jami’an tsaron farin kaya, SSS su ka mamaye hedikwatar CBN tare da mamaye ofishin Emefiele a jiya Litinin da yamma.

Ko da ya ke kakakin SSS, Peter Afunanya, ya musanta “mamayar” kuma ya bayyana rahoton a matsayin labaran karya, wasu majiyoyi masu inganci a CBN sun tabbatar da rahoton mamayar, tare da harba hotunan

Emefiele, wanda ya tafi hutu a watan Disamba 2022, ya koma bakin aiki a jiya Litinin ɗin, 16 ga watan Janairu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi, ya fitar, ta ce “gwamnan ya koma da sabon kuzari don gudanar da aikinsa gabanin taron kwamitin kula da harkokin kudi na farko, MPC, na shekarar da aka shirya yi daga ranar 23 zuwa 24 ga watan Janairu, 2023.

“Mr Emefiele ya ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikin da ke gabansa daidai da rantsuwar da ya yi da kuma manufofin Shugaba Muhammadu Buhari,” in ji Nwanisobi.

Yayin da ya ke gode wa jama’a bisa yadda su ka yi imani da bankin, babban bankin ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba wa manufofin bankin goyon baya da nufin tabbatar da ingantaccen tsarin hada-hadar kudi da tattalin arzikin ƙasa baki daya.