Home Labarai Bayan Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, layika sun dawo gidajen mai a faɗin Nijeriya

Bayan Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, layika sun dawo gidajen mai a faɗin Nijeriya

0
Bayan Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, layika sun dawo gidajen mai a faɗin Nijeriya

Sa’o’i kaɗan bayan rantsar da sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda a cikin jawabinsa ma rantsuwa ya bayyana cewa zai cire tallafin man fetur gaba dayan sa, layukan mai sun fara dawowa a faɗin Nijeriya.

Tuni dai ababek hawa su la fara kafa dogayen layika a gidajen mai a faɗin ƙasar nan, inda wasu gidajen man kuma su ka kasance a kulle.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa wadanda kuma su ka bar gidajen man su a bude amma kuma sun kara farashin lita sama da yadda gwamnatin tarayya ta amince.

Hakan ba ya rasa nasaba da rige-rigen siye na man da al’umma ke yi gabanin cire tallafin, inda a yanzu haka har farashin lita ya kai wajen Naira 350 a wasu gidajen man.

Tuni dai al’umma su ka fara ƙorafi da shakku kan mulkin Tinubu, inda su ke ganin cewa ya fara mulki da wahalar man fetur.

Sai dai kuma Kamfanin Mai na NNPCL ya bayyana cewa akwai isasshen mai a kasar, inda ya yi kira ga al’umma da kada su firgita.

Daily Nigerian Hausa ta tuntubi Shugaban Kungiyar Dillalan Mai ta Ƙasa, IPMAN, shiyyar Kano, Alhaji Bashir Ahmad Dan-Mallam, ya ce za su shiga wata ganawa ta gaggawa, inda ya tabbatar da cewa zai tuntube mu idan sun gama ganawar.