
Sarkin Daura, Umar Faruk Umar ya naɗa Yusuf Buhari, ɗan gidan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin Talban Daura.
A watan Agusta na shekarar 2019, Sarkin Daura ya naɗa Shugaban Kasar Gini na wannan lokacin, Alpha Conde a matsayin Talban Daura.
Bayan ya naɗawa Conde rawanin Talban Daura, Sarkin ya kuma kyautar doki, takobi da shanu, inda ya ce ya cancanci tagomashin sakamakon kaunar da ya ke yinwa Buhari.
Duk da cewa har yanzu Shugaban Kasar Gini ɗin ne mai riƙe da sarautar, a watan Satumbar nan kuma sai Sarkin ya sanar da cewa ya naɗa Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura.
A yau ne a ka yi gagarumin bikin naɗin sarautar a fadar Sarkin Daura.
A wajen bikin, Sarkin ya baiyana cewa an naɗa Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa sakamakon irin ci gaban da mahaifinsa ya kawowa garin Daura.
Ya yi bayanin cewa ɗan gidan Shugaban Kasar zai rika zuwa masarautar Daura a -kai -a- kai domin bada gudunmawar sa a wajen ci gaban garin.
Waɗanda su ka halarci bikin sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osibanjo, Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnan Kano da na Katsina da dai sauran manyan baƙi.