
Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Bode George, ya ce dole ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jira har zuwa 2031 idan ya na son kara yin takarar shugaban kasa.
Idan za a iya tunawa dai, Atiku yasha kayi a hannun shugaban kasa Tinubu a zaben shekarar 2023.
Mista George, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce dole ne dan kudancin kasar nan ya mulki Nijeriya daga 2023 zuwa 2031 inda ya ce “Saboda haka kundin tsarin mulkin PDP da zaman lafiyar mu ya nuna”.
“Duk da a 2027, zai cika shekaru 81, wannan ne lokacin da yakamata yayi koyi da shugaba Joe Biden ta hanyar baiwa matasa dama su yi takara.
” Bani da wani na kiyayya tsakani na da Alhaji Abubakar. Abokina ne amma dole ne a fadi gaskiya. Nan da 2027, idan Allah yaso zai kai shekaru 80.
“To me nake nema, a kujerar shugabanci a yayin da na kai gargara? Irin hakan yakamata Atiku yayi.
” Dukkan mu munga yadda Joe biden ya janye takara tare da goyan bayan Kamala Harris a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba a kasar.
“Wannan shi ne dattijantaka da Atiku yakamata yi irinta a 2027, PDP za ta tsayar da dan kudu ne takara a 2027”, inji George, tsohon Gwamnan soja na jihar Ondo.