
Hon. Bello Mawallen Maradun Dan takarar Gwamnan jihar Zamfara a karkashin tutar Jam’iyar PDP ya lashe Zaben fidda gwani na takarar Gwamnan jihar inda ya samu Kuri’u 1426.
Yayin da abokin hamayyarsa Hon. Ibrahim Shehu bakauye bai samu kuri’a ko daya ba a zaben fidda gwanin da aka bayyana sakamakonsa yanzu a Gusau babban birnin jihar.