
Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce attajiri mafi arziki a duniya Elon Musk ya sayi kamfani (Twitter) mafi girma da ke yaɗa ƙarairayi a duniya.
Biden ya yi kalaman ne daidai lokacin da Mista Musk ya kori kusan rabin ma’aikatan kamfanin Twitter cikin ƙanƙanin lokaci.
Mista Musk ya sayi kamfanin da bashi ya yi wa katutu a makon da ya gabata kan dala biliyan 44, kuma ya wallafa a shafinsa na dandalin cewa ba shi da wani zaɓi sama da ɗaukar matakin a daidai lokacin da yake asarar kusan dala miliyan huɗu a rana ɗaya.
Wakilin BBC ya ce da alama Twitter ba zai ci gaba da cire kalaman ƙiyayya da labaran ƙarya a dandalin kamar yadda ya yi a baya.
Musk ya sanar da cewa tuni manyan kamfanoni suka dakatar da bai wa Twitter tallace-tallace saboda fargabar rashin sanin inda ya dosa.