Home Ƙasashen waje Biden zai yi tazarce — Kamala Harris

Biden zai yi tazarce — Kamala Harris

0
Biden zai yi tazarce — Kamala Harris

 

 

Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta yamutsa hazo a yau Laraba game da aniyar Shugaba Joe Biden na sake tsayawa takara a shekara ta 2004, inda ta yi mi’ara-koma-baya a kan wani bayani da ta yi a farkon mako.

“Shugaban na da niyyar tsayawa takara kuma idan ya tsaya, ni ce abokiyar takararsa.

“Tare za mu yi takara,” Harris ta gaya wa wakilin LA Times yayin da ta ke shirin tashi zuwa California a cikin jirgin Air Force Two.

Masu ba da shawara sun gaya wa ɗan jaridar cewa Harris yana so ya zo bayan jirgin don fayyace abin da ta gaya wa CNN ranar Litinin.

A cikin wata hira da Dana Bash na CNN, an tambayi Harris game da raɗe-raɗin cewa Biden ba zai tsaya takara ba kuma da yiwuwar takararta.

“Joe Biden zai sake tsayawa takara, kuma ni ce abokiyar takarar sa,” Harris ta shaida wa CNN.