Home Labarai Bikin Kirsimeti: Ƙungiya ta ciyar da ƴan sanda da waɗanda a ke zargi da laifuka a Legas

Bikin Kirsimeti: Ƙungiya ta ciyar da ƴan sanda da waɗanda a ke zargi da laifuka a Legas

0
Bikin Kirsimeti: Ƙungiya ta ciyar da ƴan sanda da waɗanda a ke zargi da laifuka a Legas

 

Wata ƙungiya mai zaman kanta, mai suna Gidauniyar Taimakon Marasa Ƙarfi ta Britaniya ta ciyar da ƴan sanda da waɗanda a ka tsare a caji-ofis bisa zargin aikata laifuka har sama da guda 100 a Jihar Legas a jiya Litinin.
Ciyarwar, in ji mai ƙungiyar, Evans Uchendu, an yi ta ne albarkacin bikin Kirsimeti.
Uchendu, wanda ya jagoranci ma’aikatansa zuwa caji-ofis daban-daban, ya ce ya raba abincin ne domin ya farantawa al’umma.
“Mun kai abincin a caji-ofis na Ijesha da Itire da kuma ɓangaren binciken manyan laifuka na layin Alagbon a Ikoyi.
“Mun bada abinci sama da guda 100 da ruwan sha mai kyau da lemuka ga ƴan sanda da kuma wadanda a ke tsare da su bisa zargin aikata laifuka.
“Har ma da kayan magunguna mu ka raba musu kamar su na’ura mai duba hawan jini da su farasitamol sannan mu ka yi addu’a da jami’an ƴan sanda mu ka kuma basu ƙwarin gwiwa kan yadda su ke aikin su na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Su ma wadanda a ka tsare ɗin mun yi musu addu’a mu ka kuma yi musu wacazi a kan su gujewa aikata laifuka,” in ji shi.
Uchendu ya ƙara da cewa shirye-shiryen da ƙungiyar ke yi yanzu shine za ta shiga ƙauyuka domin tallafawa tsofaffi, musamman waɗanda basu da ƴaƴan da za su taimaka musu.