Home Siyasa Bin shawarar Buhari ce ta sanya a ka samu nasarar Babban Taron APC, in ji Ganduje

Bin shawarar Buhari ce ta sanya a ka samu nasarar Babban Taron APC, in ji Ganduje

0
Bin shawarar Buhari ce ta sanya a ka samu nasarar Babban Taron APC, in ji Ganduje

 

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa an samu nasarar gudanar da Babban Taron APC na Ƙasa cikin lumana da nasara sakamakon bin shawarwarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar.

Ganduje ya faɗi hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yaɗa labaran Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya fitar a yau Lahadi.

Yace yin aiki da shawarar Shugaba Buhari yadda ya kamata, shi ne ya sa a ka cimma nasarar da ta sa har a ka samu sulhu tsakanin masu neman kujerar shugaban jam’iyyar ta APC.

Ganduje ya ce a wuraren da a ka kasa samu sulhu, shi ne aka yi zabe kamar yadda doka ta bukata.

“Kamar yadda kuka gani an shiga zaben Kuma an kirga kuri’u an kuma bayyana wadanda suka yi nasara a zaben,” inji shi.

Gwamna Ganduje ya yaba da cewa, a karshen taron an cimma abubuwa guda biyu, cewa, “Mun fito da sabon salon shugabanci.

Na biyu kuma wannan taron ya sa muka kara samun hadin kai da kara bunkasa kuma muna da tabbacin muna da nasara.”